WWW_Hausa_web.png

Idan tsarin kiwon lafiya ya biya bukatun mata da 'yanmata, sa'anan ne ya zama mafi kyawon tsarin na kiwon lafiya.

Don muhimmancin wannan, ki yada wadannan tambayoyi domin ki shigar da taki murya cikin muryoyin mata da 'yanmata miliyan daya a fadin duniya domin kira zuwa ga canji.

Mahangarki muhimmiya ce kuma abar lura!

Wannan shi ne dalilin da  ya sa kungiyoyi kula da lafiya da na zamantakewar al'umma a duniya baki daya, suke haduwa domin su yi tambayoyi ga mata miliyan daya, masu shekaru daban-daban da kuma 'yanmata masu shekaru 15 zuwa 19, a kan mafi girman bukatunsu a sha'anin ingancin ayyukan kulawa da  lafiya a bangare haihuwa da abin da ya shafi haihuwa.

Amsoshin wadannan tambayoyi za su taimaka wa tsare-tsare da shirye-shiryen da aikace-aikace tare da la'akari da gogewar mata da 'yanmatan wajen inganta kiwon lafiya, ba tare da la'akari da matsayi ko inda suke zaune ba. Mahangarki muhimmiya ce kuma abar lura! Don muhimmancin wannan, ki yada wadannan tambayoyi domin ki shigar da taki murya cikin muryoyin mata da 'yanmata miliyan daya a fadin duniya domin kira zuwa ga canji.  

Amsoshin wadannan tambayoyi za su taimaka wa tsare-tsare da shirye-shiryen da aikace-aikace tare da la'akari da gogewar mata da 'yanmatan wajen inganta kiwon lafiya, ba tare da la'akari da matsayi ko inda suke zaune ba.

 

Kin fi son ki rubuta amsoshinki da rubutun hannu? Akwai bangaren amfani da takarda a wannan bincike.